News
Kamfanin BUA ya sanar da ƙarin kashi 50 na albashin ma’aikata
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban Kamfanin BUA, Abdul Samad Isyaku Rabiu, ya ce kamfanin ya amince da karin kashi 50 cikin 100 kan albashin ma’aikata.
Majalisar tarayya na duba yiwuwar Karin sabbin jahohi 3 a kudu maso yammacin Nigeria
Rabiu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ta cikin gida da Mohammed Wali, shugaban sashen kula da ma’aikata na BUA ya sanyawa hannu a yau Lahadi a Legas.
Sanarwar ta ruwaito shugaban BUA na cewa an yi karin albashin ne don rage raɗaɗin tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu.
Ya ce karin albashin ya haɗa da duka ma’aikata na dindindin da ba na dindindin ba daga ranar 1 ga Fabrairu, 2024.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
