Connect with us

News

Cire tallafin fetur ya zama ciwon ido, sai haƙuri –Shugaba Tinubu

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa cire tallafin fetur ya haifar wa ‘yan Najeriya wasu wahalhalu, amma kuma ya zama tilas ta sa aka cire, domin tattalin arzikin Najeriya ya sami tagomashi nan gaba.

Shugaba Bola Tinubu ne ya bayyana haka, a ranar Talata, wurin buɗe Taron Ƙasa da Ƙasa kan Makamashi, na 7 wanda aka gudanar a Abuja, ranar Talata.

Masu gidajen Burodi sun fara yajin aiki a Nijeriya

“Ƙasaitacciyar ƙasar mu ta daɗe ta na dogaro da kuɗaɗen fetur ta hanyar fitar da shi waje. Ya zama dole mu sake duba wannan matsala, domin mu samar da ƙasaitacciyar ƙasa nan gaba kaɗan.

“Cire tallafin fetur ya zama ciwon ido sai haƙuri. Amma mun cire ne domin ganin mun maida ƙasar mu ƙasaitacciya,” Cewar Tinubu.

Tinubu wanda Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ya wakilce shi, ya ce makamashi abu ne mai muhimmanci ga kowace ƙasa, domin ta bunƙasa.

Advertisement

Ya ci gaba da cewa cikin shekarun da suka gabata, tallafin fetur ya yi wa cigaban tattalin arzikin Najeriya dabaibayi.

Hakan ya haifar da matsalolin kasa zuba jari a fannin makamashi.

“Amma yanzu da aka cire tallafin fetur, mun gina sashen samar da kuɗaɗen mai mai inganci.

“Maƙudan kuɗaɗen da a baya ake warewa ana bayarwa matsayin kuɗaɗen tallafin mai, yanzu su ne ake yin amfani da su wuraren ayyukan raya ƙasa da sauran su,” cewar sa.

Kwanan nan ne kuma Najeriya ta amince da shawarar Bankin IMF, Ministan Lantarki ya ce za a cire tallafin

wutar lantarki.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa zai yi wahala ta ci gaba da ɗaukar nauyin tallafin kuɗin wutar lantarki.

Ministan Wutar Makamashi, Adebayo Adekabu ne ya bayyana haka a ranar Laraba, lokacin da ya ke wa manema labarai bayani, yayin da ya ke amsa tambayoyi.

Adelabu ya ce ɗimbin bashin da Najeriya ke bin kamfanonin sayar da wutar lantarki (GenCos) ya ƙaru zuwa Naira tiriliyan 3.

“A yau muna bin kamfanonin samar da wutar lantarki Naira tiriliyan 1.3, daga cikin kuɗaɗen kuma kashi 60 bisa 100 na gas ne da ake sayar masu bashi.

“Sannan kuma mun gaji bashin da gwamnatin baya ke bi tun 2014 ga kamfanonin kamfanonin wutar lantarki har dala biliyan 1.3. idan an haɗa kuɗin jimilla za su kai Naira tiriliyan 2 kenan.

“To idan ka haɗa Naira tiriliyan 2 da kuɗaɗen gas Naira tiriliyan 3, muna da bashin Naira tiriliyan 3 kenan.

Advertisement

“Shin ta yaya wannan ɓangare zai ci gaba kenan? Ya kamata ‘yan Najeriya su san da wannan.

“Amma kuma muna aiki ta ƙarƙashin ƙasa domin mu tabbatar da cewa an warware wannan matsalar bashi, an biya domin a ci gaba da samun wuta.” Inji Adelabu.

Da aka yi masa magana kan tallafin wutar lantarki, ya ce ƙasashe irin su Ghana, Togo, da Jamhuriyar Benin sun fi shan wuta da tsada fiye da Najeriya.

“Naira biliyan 450 kaɗai aka ware na tallafin wuta a kasafin 2024, amma kuma Naira tiriliyan 2.9 muke nema. To ina za mu samo cikon””

Shawarar Bankin IMF:

CIkin wannan makon ne Bankin IMF ya shawarci CBN ya ƙara kuɗin ruwa, domin a saisaita tattalin arzikin Najeriya.

Advertisement

Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF) ya bijiro wa Najeriya da wasu shawarwarin da ya ce idan aka yi amfani da su, to za a hau kan turbar saisaita tattalin arzikin ƙasa.

Daga cikin shawarwarin, IMF ya ce ya kamata Babban Bankin Najeriya (CBN) ya matse hannu, ya rage sakin kuɗaɗe.

Sai dai kuma babbar shawarar da bankin ya bayar ita ce a ƙara adadin gejin kuɗin ruwa, abin da ya ce idan aka yi hakan, nan da watanni shida zuwa shekara ɗaya, lamarin zai daidaita kuma ya saisaitu.

“Ya kamata a raƙa gejin yawan kuɗin kuɗin ruwa yayin taron Kwamitin Tsara Hada-hadar Kudade (MPC), domin idan aka yi hakan, to nan da watanni shida zuwa shekara ɗaya lamarin zai daidaita.”

Haka nan kuma IMF ya bada shawarar a tatse toliyar adadin kuɗaɗen hada-hada, ta yadda daga farko za a maida hankali wajen tatse Naira biliyan 800 na rarar asusun ajiya, ta yadda a cikin shekara ɗaya za a iya tatsar har Naira tiriliyan 2.

IMF ya bada shawarar a ƙara kuɗaɗen ruwa a daidai lokacin da lalacewar darajar Naira ya kai duk Dala ɗaya kan Naira 1,534 a farashin gwamnatin tarayya.

Advertisement

PREMIUM TIMES Hausa ta buga rahoton wata shawarar janye tallafin kuɗin wutar lantarki da Bankin IMF ya ba Najeriya.

‘A cikin labarin, Bankin IMF ya shawarci Najeriya ta cire tallafin fetur kwata-kwata da tallafin kuɗin lantarki.

Bankin Dada Lamuni na Duniya (IMF), ya shawarci Najeriya ta ƙara rufe ido ta cire ɗan sauran tallafin fetur da tallafin kuɗin wutar lantarki, domin ta magance matsalolin da suka dabaibaye tattalin arzikin ƙasa.

IMF ta ce kuɗaɗen tallafin su ne ke ƙara damalmala tattalin arzikin Najeriya.

Bankin ya ce kuma wannan matsala ta tallafi ce ke ƙara rura wutar talauci da matsalar abinci.

A cikin rahoton da IMF ya fitar kan Najeriya, IMF ya bayyana muhimmancin cire tallafin fetur da na wutar lantarki domin a karkatar da maƙudan kuɗaɗen tallafin da gwamnati ke ɗaukar nauyin biya wajen yin ayyukan raya ƙasa da raya al’umma da kuɗaɗen.

Advertisement

IMF ya bayar da wannan shawara ce a halin yanzu da ake tsakiyar fama da raɗaɗin tsadar rayuwa da masifar tsadar kayan abinci, wadda ba a taɓa fuskantar irin ta ba a tarihin Najeriya.

Amma kuma IMF ya bada shawarar cewa gwamnati ta ɗan yi wa marasa galihu wani ɗan ihisanin rage masu raɗaɗin tsadar rayuwa.

“Tallafin fetur da tallafin kuɗaɗen wutar lantarki waɗanda gwamnati ke biya, talakawan da ake yi don su ba su samun alfanun abin. Don haka a cire tallafin kwata-kwata. Amma gwamnati ta yi wa marasa galihu ɗan ihisanin rage masu raɗaɗin tsadar rayuwa, bisa la’akari da halin tsadar kayan masarufin da ake fama da shi.” Inji IMF.

Najeriya ta cire tallafin man fetur a ranar 29 ga Mayu, 2023 da nufin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da kuɗaɗen. Lamarin dai ya haddasa mummunar tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci wanda ba a taɓa fuskanta ba.

Wannan masifa ta kai ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bayyana wasu shirye-shiryen rage raɗaɗin tsadar rayuwa, amma har yanzu shiru talaka bai ga komai a ƙasa ba.

Yayin da gwamnatin tarayya ke ƙara samun kuɗaɗen shiga a kullum fiye da lokacin gwamnatin Buhari, an rasa abin da ake yi da kuɗaɗenz ganin yadda a kullum kuma gwamnatin da ‘yan Najeriya sai ƙasa nausawa cikin masifar durƙushewar tattalin arzikin ƙasa da tsadar rayuwa ake yi.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya ta kasa biyan albashin ma’aikata na watan Janairu kan lokaci, har sai da ta kai w

asu yawancin ma’aikatun ma sai a ranar 8 ga Fabrairu ko 9 ga wata suka ji ‘alat’

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending