Connect with us

News

Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi awon gaba da wasu masallata  cikin masallacin a Zamfara.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi awon gaba da wasu masallata a ɗaya daga cikin masallacin da ke garin Tsafe hedikwatar ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Wani ɗan yankin mai suna Garba ya bayyana cewa ƴan bindigar sun mamaye masallacin ne da misalin karfe 5 na safiyar ranar Alhamis a lokacin da mutanen ke shirin fara Sallar Asuba.

Kada ku rasa wannan damar, saka hannun jari Yanzu A company BAHAL DATA Ga dama ta samu 

Garba ya ce, “Yau alhamis muna shirin tada sallar asuba, kwatsam sai ga yan bindiga sun dira masallaci inda suka umurci duk jama’an ciki su biyo su inda Ni na yi nasarar ɓoyewa ba su ganni ba.”

Ya ƙara da cewa saboda kar a ji karar abin bawan su sai suka ajiye Baburan su can nesa.

Advertisement

A ƙalla mutane 30 ne aka yi awon gaba da su.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending