News
Yadda gwamnatin Kano da ɗan Majalisa Ado Doguwa suka yi watsi da mutanen Tudunwadan Ɗankadai, rashin ruwa na neman ya hallaka su
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI TUKUNTAWA
A yayin da al’umma ke ta gudanar da ibadar azumin watan Ramadan, Al’ummar ƙaramar hukumar Tudunwadan Ɗankadai a jihar Kano, na fama da matsalar tsananin rashin ruwan sha a yankin.
Wannan matsala dai ba tun yanzu ne al’ummar ke fama da ita ba, a wannan karon ta yi munin gaske musamman a yanzu da ake cikin watan Azumi, mutane na buƙatar ruwan sha da amfani.
Ana Tsaka Da Azumi Wani Ya Ɗirkawa Ƴar Shekara 9 Fyaɗe Kuma Ya Kashe Ta
Mazauna Tudunwadan Ɗankadai sun shafe shekaru da dama suna fama da tsananin rashin ruwan sha.
PREMIUM TIMES HAUSA ta tattauna da wasu mazauna wannan gari inda suka bayyana rashin jin daɗin su game da wannan matsala da suke fama ita sannan kuma ta ki ci taki cinyewa har yanzu.
Idris Abdullahi, mazaunin garin ya shaida wa wakilinmu cewa lamarin ya yi matuƙar muni, kuma mutane na wahalar da ba shi misaltuwa.
” Mutane na cikin tsananin wahala a wannan gari na Tudunwadan Ɗankadai. Babu ruwa daidai na sha babu, mutane kan garzaya koramu ne suna kwalfo ruwa, haka zaka ga ruwan jajawur, sannan duk da rashin kyan ruwan haka suka ɗiba su yi amfani da su.
Wasu kuma sun koka da yadda gwamnatin Kano na baya da na yanzu suka yi watsi da mutanen yankin wajen kawo musu ɗauki da kuma warware matsalar ruwan sha a wannan yanki.
Mutanen garin sun shaida cewa sun mika koken su ga ɗan majalisar tarayya dake wakiltar yankin Alhassan Ado Doguwa sai dai hakan bai haifar musu da ɗa mai ido ba.
” Ado Doguwa ne ke wakiltar mu a Abuja, kuma an mika masa koken mu amma bai yi komai akai ba, gwamnatin Kano ita ma bata yi komai akai ba, mutane kuma na dandana wahala saboda ruwan sha.
A karshe sun roki gwamna Kabir Yusuf na Kano da ya kawo wa wannan ƙauye ɗauki na gaggawa a samu a samar wa mutane yadda za su rika samun ruwan sha da na amfani ba tare da suna wahala irin haka ba.
