Connect with us

News

A Cikin Watanni 2 Yan Kasuwar Magani Sunyi Asarar Miliyoyin Kudi Tare Da Rasa Aikinyi A Kano  —Shugaban Yan Kungiyar Yan Magani

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Yan kasuwar magani da ke jihar Kano sun gudanar da tattakai zuwa fadar gwamnatin jahar Kano a ranar litinin, kan yadda suka ce an tilasta musu tashi daga kasuwar su da kuma kulle musu shaguna.

Shugaban Yan kungiyar yan maganin Alhaji Musbahu Yahaya Khalid ne ya jagorancin tattakai lumana inda suke kira ga gwamnati da tayi duba da irin halin matsi da suke ciki a wannan lokaci wajen kawo musu daukin gaggawa.

Dan takarar jam’iyya mai mulki a Senegal ya amsa shan kaye a zaben shugaban kasa

Alhaji Musbahu Yahaya ya ce dalilin su na kin amincewa da komawa kasuwar Dangoro shi ne, la’akarin da yadda kasuwar da Dangoro ta kasance mallakin su mutane ba ta gwamnati ba kuma adadin shagunan da suke wajen bazasu ishi yan kasuwar ba, da a kalla sun kai sama da 3000 su da suke gudanar da kasuwancin na magani kuma ita wannan kasuwar shagunan cikin ta basu huce 600 ba.

Ya ce sunje wajen gwamnan jahar Kano Engr. abba Kabir Yusuf, a matsayin sa na shugaban rundunonin tsaro, ya shiga cikin lamarin don a bude mu su shagunan su.

“Mu muka kafa wannan gwamnatin da gumummu, karfe ukun dare Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce mu fito mu tafi INEC kuma muka je aka tabbatar , haka ana shari’a tun daga Kano muke bin shari’ar babu wajen da ba muje munyi sallah ba , don ya samu nasara a kotu, ko shaida ne da aka samu nasarar mun kashe kudi sama da naira miliyan biyar , wajen taron Gwamna Abba Kabir Yusuf, Wanda muke zaton zai yi abubuwa na alkairi sai kuma aka Fara zungure mu”. Musbahu Khalid”.

Advertisement

“A dan haka idan gwamnati zata shiga lamarin ya kasance kasuwar a hannun gwamnati take su a shirye suke su koma amma a yanzu kudin da aka sanya a matsayin kudin haya yayi yawa la’akari da yadda akace koya sai ya biya

miliyan 3 kudin haya maimakon Dubu 300 zuwa Dubu 500 da suke biya A cewar Shugaban”

A kwanakin baya ne Wata babbar kotun tarayya a birnin Kano, ta umarce su da su tashi, su koma kasuwar Dangora a yankin karamar hukumar Kumbotso.

Ana zargin Yan maganin da shigo da gurbatattun magani, da miyagun kwayoyi, zargin da suka sha musanta wa.

Ma su sharhi kan al’amuran yau sa Kullum na ganin kokawar Yan maganin kasuwar Dangoro, ba zai haifar da Da mai ido, bisa zargin za a Samu yawaitar siyar da magungunana unguwanni.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending