News
An gyara tashoshin samar da wutar lantarki da suka daina aiki a Najeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kamfanin samar da wutar Lantarki na Kasa ya bayyana cewa an gyara tashoshin wutar lantarki da suka daina aiki jiya a Najeriya.
Kamfanin ta ce tun da misalin karfe 10 na dare ranar Alhamis aka gyara komai suka koma aiki wurjanjan.
Babbar Magana: Kwalejin Koyon Tuƙin Jirgi ba ta da jirgin koyon tuƙi ko ɗaya – Shugaban Kwajeli
Premium Times ta ruwaito cewa Manajan hulda da jama’a na kamfanin Ndidi Mba, ta ce rashin isasshen iskar gas ne ya sa aka samu wannan matsala a ranar Alhamis.
Najeriya ta fada cikin duhu a ranar Alhamis da yamma bayan daina aiki da babbar tashar samar da wutar lantarki da ke Osogbo na jihar Osun ya yi.
Wata majiya a daya daga cikin kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCo) kusan duka inda ake samun wutar lantarki a kasarnan ba su da wuta kwata-kwata da hakan ya shafi duka jihohin kasarnan ne 36 kaf.
Tasha daya ce ke da wuta har megawatt 54 kacal a faɗin kasar nan.
