News
Rundunar Ƴan Sanda Ta Kama Mutum 4 Bisa Yinkurin Ƙona Sansanin Ƴan Gudun Hijira
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta gurfanar da wasu mutane huɗu da ake zargi da yunƙurin cinna wuta a sansanin yan gudun hijira da ke Mafa a jihar Borno.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa sunayen waɗanda ake zargin su ne Malum Usman mai shekaru 16; Bulama Bukar, 14; da Rawa Usman, 11; wanda ake zargin wani Babagana Umar mai shekaru 40 shi ne ya ɗauki nauyinsu.
An sami rahoton ne a lokacin da wata kungiyar mafarauta a Mafa ta kai rahoto ga ƴan sanda cewa an kama waɗanda ake zargin da ashana a lokacin da suke kokarin bankawa wani gida wuta a sansanin ƴan gudun hijira a ranar 24 ga watan Maris, 2024, da misalin karfe 10:30 na safe.
ASP Kenneth Nahum Daso, ya ce sun gano cewar Babagana Umar ya ce zai biya waɗannan yara kuɗi Naira 10,000.Sai dai wanda ake zargin ya musanta.Inda yanzu haka ƴan Sanda na gudanar da bincike.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News4 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
