Connect with us

News

Gwamnati ta hana ‘yan sanda yin kutse cikin wayoyin mutane lokacin sintiri

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Edo Funsho Adehboye ya hana ‘yan sanda kwacewa da duba woyoyin hannu na mutane yayin da suke sintiri a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Chidi Nwabuzor ya sanar da haka a shafin sada zumunta na rundunar dake yanar gizo a makon jiya.

Watanni Takwas Na Farkon Gwamnatin Mu Sun Fi Shekaru Takwas Na Mulkin Ganduje — Abba Kabir-Yusuf

“Kwamishinan ‘yan sandan jihar Edo ya gargadi jami’an rundunar da su daina wannan aika-aika, domin babban sufeton ‘yan sandan ya umarci kwamishinoni da AIG na shiyoyi da su sanya ido kan ma’aikatansu.

Premium Times ta ruwaito cewa wannan umarnin da kwamishinan ya bada ya biyo bayan watanni biyu da kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas ya bada umarnin irin haka a jihar.

Rundunar ta bada wannan umarnin ne bayan korafin da mutane suka yi na yadda jami’an tsaro ke yi musu kutse a cikin wayoyin su da karfin tsiya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending