Connect with us

News

Hukumar EFCC Ta Je Kama Tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Jami’an Hukumar Yaki da masu karya tattalin arziki (EFCC) sun kai samame gidan tsohon gwamnan jihar Kogi Bello da ke Abuja.

Wakilin jaridar Daily trust ya is layin Benghazi a unguwar Wuse da gidan na Yahaya Bello yake, inda ya ga jami’an na EFCC.

Yadda Sauraron Ƙarar Da Gwamnatin Kano Ta Shigar Kan Ganduje Ta Kasance.

Wani babban jami’in EFCC da ya bukaci wakilin namu ya sakaya sunansa ya tabbatar cewa sun kai samamen ne da nufin kama da Yahaya Bello.

Sai da kuma jami’in ya ki amsa tambayar wakilin namu game da zargin da hukumar ke wa tsohon gwamnan.

Ana dai tunanin samamen na da alaƙa da badaƙalar Naira biliyan 84 na jihar Kogi a zamanin mulkin Yahaya Bello da EFCC ke bincike a kai.

Advertisement

Kokarin wakilinmu na samun karin bayani daga kakakin EFCC, ya ci tura.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending