News
‘Yan Sanda Sun Kama Matar Da Ta Yi Karyar Garkuwa Da Ita Sannan Ta Yi Wa Kanta Farashin Kudin Fansa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar ‘yan sanda a jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya, ta kama wasu mutane uku da ake zargi masu garkuwa da mutane ne, ciki har da wata mata da ta yi karyar sace ta sanna ta yi wa kanta kudin fansa har Naira miliyan 4.8.
A cikin wata sanarwa da aka buga a ranar Litinin, mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar, Chidi Nwabuzor, ya ce an kama su ne ta dabara amfani da fasahar zamani.
Yanzu-yanzu:Wata Hatsaniya Ta Kaure Tsakanin Sojoji Da yan Adai-daita sahu
Nwabuzor, Sufeton ‘yan sanda, ya bayyana matar da Blessing Ogunu, ma’aikaciyar Bliss Legacy Limited da ke garin Benin.
Sauran wadanda ake zargin su ne Esther Anthony da Ukpebor Joel.
“Lokacin da ake yi mata tambayoyi, Blessing Ogunu ta amsa cewa ta shirya duk yadda aka yi garkuwa da ita ne saboda kamfaninta ya ki bai wa wani mutum fili da suka karbi kudi a wurinsa.
Premium Times ta ruwaito cewa Kwamishinan ‘yan sandan ya ce wanda ake zargin, ya amsa laifin hada baki da saurayin ta da wasu mutane uku wajen yin garkuwa da ita, domin samun kudi a hannun ‘yar uwarta dake zaune a kasashen waje.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
