Connect with us

News

Iran ta musanta iƙirarin kai mata harin ‘makamai masu linzami

Published

on

DAGA NASIRU ADAMU 

Wani jami’in gwamnatin Iran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa babu wani harin makamai masu linzami da aka kai a cikin ƙasarsu, yana mai ƙaryata rahotannin kafafen watsa labaran Amurka da ke cewa Isra’ila ta kai musu hari.

Advertisement

An ambato kakakin hukumar kula da sararin samaniyar Iran yana cewa ba a kai musu harin makamai masu linzami ba, inda ya ƙara da cewa na’urorinsu sun kakkaɓo jirage maras matuƙa da dama daga sararin samaniyar yankin Isfahan.

Atiku Da Wike Sun Hadu Karon Farko Tun Bayan Zaben 2023

Sai dai jami’an gwamnatin Amurka biyu sun tabbatar wa CBS News cewa wani makami mai linzami na Isra’ila ya sauka a Iran. Reuters ya ruwaito cewa Isra’ila ta gaya wa Amurka shirinta na kai wa Iran hari.

Advertisement

Wasu jami’an gwamnatin Amurka da ba sa so a ambace su sun shaida wa CBS News cewa Isra’ila ta yi amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango a harin da ta kai wa Iran.

Wani jami’in Amurka ya shaida wa CNN cewa mahukunta a Washington ba su “amince” Isra’ila ta kai harin ba.

Advertisement

 

Trt Afrika 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending