Connect with us

News

Ya Kamata Gwamnati Ta Fara Tilastawa Yan Kasuwa Da Kamfanoni Masu Tsauwalawa Al’umma Don Su Sauke farashin kayan su —Amb Auwalu Muhd Danlarabawa 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Shugaban Gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe wato Grassroot Care and Aid Foundation Amb. Auwalu Muhd Danlarabawa, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da dukkan zababbun gwamnatocin jihohi da su yi kira ga Yan kasuwa domin su sauke farashin kayayyakin su ko kuma su dauki matakan gaggawa da suka dace akan su.

Advertisement

Amb Auwalu Muhd Danlarabawa yayi wannan Kiran ne yau a wajen wani taro da ya shirya na bawa Mata iyayen Marayu 300 masu Sana’a jari, Wanda gidauniyar take bayarwa a kowanne lokaci Dan Tallafawa matan su tsaya da kafafunsu sannan su kula da Rayuwar Marayun da aka Mutu aka bar musu.

Karatun Fatiha Ya Jawo Wa Jarumin Tik-Tok G-Fresh Caccaka

Amb Danlarabawa ya Kara da cewa tabbas Al’umma suna cikin wani hali tun lokacin da Dala ta tashi, mussaman yadda farashin kayan Masarufi sukai tashin gauron zabi a fadin Najeriya Wanda har yanzu ana cikin wannan yanayin ba canji”.

Advertisement

 

Talakawa sun shiga wani hali na matsin rayuwa saboda yadda ake maganar Dala tayi tashin gauron zabi, sai gashi kuma yanzu Dala ta sauko, to shin mai ya kamata Yan kasuwar mu da kanfanoni da suke bawa Yan Kasuwar Kaya suyi a yanzu? Shi ne su sauke farashin kaya domin Talaka ya samu sauki”.

Advertisement

 

Amb Auwalu Muhd Danlarabawa Sarkin Zaman Lafiya Yace duk dan kasuwar da zai yi ikirarin cewar Dala ta tashi zai kara kudin kaya, to ya kamata tunda yanzu Dala ta sauko ya sauke farashin kayansa idan har da gaske yake.

Advertisement

 

“Muna kira ga gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusif yadda ya zauna da Yan kasuwa a baya, da yanzu ma ya taimaka ya zauna da su domin talakawa su samu saukin halin da suke ciki”. Sannan sauran gwamnonin Suma suyi haka a wasu jahohin da muke dasu a kasa, A cewar Amb Auwalu Muhd Danlarabawa

Advertisement

 

Hatta gwamnatin tarayya muna kira gare ta da tayi abinda ya dace akan Yan kasuwar mu, domin tabbatar da cewa sun sauke farashin kayansu, wanda ya hada da batun gas da man fetur, Dan wannan hakki ne da ya wajaba akansu Kuma al’umma su samu intacciyar rayuwa Mai kyau a zauna lafiya a kasa.

Advertisement

 

Jefa al’umma a mummunan yanayi Yana Haifar da tashin hankali da aikata mummunan laifuka a kasa Wanda Daga Nan Kuma baa San me zai faru ba,. Dan kowa na Neman tsira da rayuwa zukata na iya aikata kowanne irin laifi a sakamako wahala da tsadar rayuwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending