News
Babbar Magana: Wani Mutum Ya Kashe Matarsa Da Dutsen Guga A Kano
DAGA MUHAMMAD BASHIR MUSA
Kotun majistre mai lamba 26 ta aike da wani magidanci Adamu Ibrahim gidan yari bisa zarginsa da hallaka mai matarsa ta hanyar buga mata dutsen guga a fuska.
Jaridar Bustan Daily ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a garin Kwanar Dangora da ke karamar hukumar Kiru ta Jihar Kano.
Acewar Adamu sabani ne ya shiga tsakaninsa da matarsa dalilin wata mata da ta nuna ba ta son mu’amalarsa da ita.
Sai dai ya ce ya yi ƙoƙarin fahimtar da ita, amma abin ya ci tura, inda ta ce babu ita babu zama da kishiya.
Daga nan ne a cewarsa ta kama shi da kokawa, kuma duk da ihun da yake yi ta ki rabuwa da shi, har ya aikata abinda ya aikata
Share this:
-
News3 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News4 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
