Business
Kamfanonin Sadarwa A Nijeriya Na Neman Sahalewar Gwamnatin Domin Kara Kudin Kiran Waya.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kamfanonin sadarwa na Najeriya da suka hada da Glo, MTN, Airtel, da 9Mobile, suna kira ga gwamnatin tarayya sun shiga tattaunawa neman sahalewar gwamnatin domin kara kudin kiran waya tare magance kalubalen tattalin arziki.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da kungiyar kamfanonin sadarwa ta Najeriya ALTON da kungiyar kamfanonin sadarwa ta Najeriya (ATCON) suka fitar, kamfanonin sun bayyana damuwarsu da cewa su kadai ne ba su gyara farashin su ba, wanda hakan na iya kawo cikas ga harkokin masana’antar kuma dorewa da kuma lalata amincewar masu saka jari.
Tsananin Zafi: Dakta Labaran Buƙaci Mutane su Ɗauki Matakan Kariya na Kiwon Lafiya
Jaridar Tribune ta ruwaito cewa Shugaban ALTON, Mista Gbenga Adebayo, da Shugaban ATCON, Mista Tony Emokpere, sun bayyana cewa, ba a sake yin wani bita a cikin tsarin farashin hidima na gama-gari a cikin shekaru 11 da suka gabata, saboda matsalolin da suka shafi doka, duk da matsalolin tattalin arziki.
Sanarwar ta jaddada bukatar samar da tsarin farashin da zai daidaita karfin masu amfani da kudin da masu gudanar da harkokin kudi tare da yin kira ga gwamnati da ta saukaka tattaunawa don magance wadannan kalubale.
-
News1 day ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
