Connect with us

News

Akalla Yara 19 Suka Rasu Sanadiyyar Kamuwa Da Cutar Kyanda A Adamawa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

A kalla yara kanana 19 ne suka rasu sanadiyyar kamuwa da cutar Kyanda  a karamar hukumar Mubi, dake  Jihar Adamawa.

Kwamishinan lafiya na jihar Felix Tangwami ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a Mubi ranar Asabar cewa sama da yara 200 ne suka kamu da cutar a karamar hukumar.

Yadda Ɗan Shekara 12 Ya Bindige Ƙanin Sa Dan Shekara 6 Bisa Kuskure A Taraba – ‘Yan Sanda

Ya ce an soma samun labarin barkewar cutar ce a garin Yola, inda cikin gaggawa aka tura jami’an lafiya da magunguna domin a taro cutar kada ta yi ɓarkewar da ba za a iya shawo kansa da wuri ba.

Ya kuma ba da tabbacin cewa za a mika yaran da suka kamu da cutar zuwa snyan asibitocin jihar domin a basu kula.

Premium Times ta ruwaito cewa Kwamishinan ya ce tawagar likitocin za su kuma nausa zuwa karamar hukumar Gombi inda aka sake samun bullar cutar.

Advertisement

A karshe Tangwami ya dora laifin kin kai yara asibiti a yi wa ‘ya’ya rigakafin citar tun farko ne yi sanadiyar samun ɓarkewar cutar a yankunan jihar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending