News
Karnuka Sun Cinye Sassan Jikin Jaririya sabuwar haihuwa da aka jefar a Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A ranar Alhamis da karfe 6:50 na safe ne aka wayi gari da ganin gawar wata Jaririya sabuwar haihuwa da aka jefar a Unguwar (Gaida Maharba) Layin Sabis da ke Karamar Hukumar Kumbotso a jihar Kano.
Rahotanni na nuni da cewa Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da al’umma suka fara futowa daga gidajensu, inda suka iske gawar jaririyar a bakin hanya.
Saidai wasu shaidun gani da ido sun bayyana lamarin a matsayin rashin imani da tausayi wanda ake kyautata zaton cikin dare aka bi aka jefar da jaririyar.
Jaridar SolaceBase ta tuntubi mai unguwar yankin, Malam Saleh Sa’idu, kan sahihancin lamarin, mai unguwar ya tabbatar da cewar tabbas lamarin ya faru kuma shi ma ya kadu da ganin gawar sabuwar jaririyar.
“Tabbas wannan lamari ya faru kuma ni kaina nayi matukar kaduwa da tashin hankali dana iske wannan lamari da idanu na.
“Bayan faruwar lamarin, na yi kokarin sanarwa da Dagachi da Hakimi, sannan na yiwa jami’an tsaron ‘yan sanda na Panshekara karin haske dangane da lamarin, wanda daga nan ne suka ba da damar yiwa gawar sutura”.
Sa’idu, ya kara da cewa, “Wannan karo na uku kenan ana ganin makamancin irin wannan rashin imanin a yanki na, amma dai na yanzun yafi kowanne muni sosai fiye dana baya.”
Sai dai a karshe, Saleh, ya bayyana ba’a tabbatar da wadanda suka aikata wannan danyen aikin ba, amma dai sun barwa jami’an tsaro da kwamitin unguwa komai a hannunsu domin ci gaba da yin buncike
“Har yanzu ba’a tabbatar da wadanda suka aikata wannan danyen aikin ba, amma mun barwa jami’an tsaro da kwamitin unguwa komai a hannunsu domin ci gaba da yin buncike kan wannan mummunar lamarin” in ji Mai Unguwar.
Ba wannan ne karo na farko da ake ganin jarirai musamman sabbin haihuwa a wasu yankuna na birnin Kano da wajen birnin ana jefar da su ba, ana tsintar wasu da ransu wasu kuma a tsinci gawarsu ne.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
