News
Darajar takardar kudin Naira ta sake komawa cikin mawuyacin hali
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kasa da makonni uku da taka rawa mafi inganci a fannin kudi a duniya, darajar takardar kudin Naira ta sake faduwa kasa warwas, inda ake sayan kowanne Dalar Amirka daya a kan 1415 na Naira a halin yanzu.
A cikin kibtawa ta bisimillah ne Naira ta tarayyar Najeriya ta rikide daga kudi mafi taka rawa mai kyau a duniya ya zuwa ta kan gaba a fannin lalacewa. Rushewar kudin kasar daga kasa da Naira 1000 makonni uku baya ya zuwa Naira 1416 kan kowace Dala dai, ya tada hankalin ‘yan mulkin tarayyar Najeriya da ke ta tsallen murnan kai karshen rikicin na kudi. Abin da ya kai hukumar EFCC da aiwatar da wani samame zuwa ga kasuwar ‘yan canji da ke a Abuja.
Akalla masu canjin biyu ne aka kame bayan daruruwan miliyoyi da jami’ai na hukumar EFCC suka kwashe bayan harbi da bindiga. Abdullahi Abubakar Daura da ke zaman shugaba na kungiyar ‘yan canjin ta Abuja ya ce lamura sun koma dai ai bayan samamen da ya kai ga tada hankali na matasan ‘yan canji.
A baya, babban bankin kasar na CBN ya dauki jerin matakai da nufin sake farfado da darajar Naira da nufin kawo karshen hauhawar farashin da tsadar kudaden kasashen waje da ke zaman barazana mai girma a ckin kasar. Duk da cewar a takarda, bankin ya bayyana tsoma baki tare da fitar da darururwan miliyoyi na daloli da nufin tallafa wa Nairar, amma ga dukkan alamu akwai sauran tafiya a tsakanin kasar Najeriya da kaiwa ya zuwa sauke farashin.
Ana Kallon kokari na karfin hatsi a matsayin alamu na gazawar mahukuntan Abuja da ke tunanin mafitar a cikin halin rudu. Umar Garkuwa ya share lokaci yana sana’ar canjin, kuma ya ce da kamar wuye batun murde wuyar ‘yan canjin ya kai ga sake dora Nairar bisa hanyar girma. Tun ma kafin far wa masu takama a sana’ar canjin dai, an yi nisa a kace-nace tsakanin mahukuntan kasar da kamfanonin da ke hada-hadar kudi na fasaha ta zamani.
