News
Gwamnatin Jihar Kogi ta tabbatar da ceto ɗaliban da aka sace daga Jami’ar Confluence.
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Gwamnatin Jihar Kogi ta tabbatar da ceto wasu daga cikin ɗaliban da aka sace daga Jami’ar Confluence da ke jihar.
A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar a ranar Lahadi, ta tabbatar da cewa ‘yan bijilanti da taimakon jami’an tsaro ne suka yi aikin ceto ɗaliban.
Darajar takardar kudin Naira ta ta sake komawa cikin mawuyacin hali
Gwamnatin ta ce wani ɗan bijilanti da jami’in hukumar DSS sun jikkata a yayin musayar wuta da masu garkuwar, amma a halin yanzu suna samun kulawa a asibiti.
Haka ma gwamnatin ta ce ɗaliban da aka ceton su ma an kai su asibiti domin duba lafiyarsu.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
