Connect with us

News

Yadda Ƴan ta’adda suka dagargaza ƙauyuka 50, suka sace daruruwan mutane a Zamfara 

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Ƴan ta’adda sun kori kimanin al’ummomi 50 tare da yin garkuwa da daruruwan mazauna yankin bayan shafe makonni ana kai hare-hare a karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara, kamar yadda wani dan majalisa daga yankin ya bayyana.

Advertisement

Premium Times ta ruwaito cewa Bello Hassan, wanda ke wakiltar mazabar Zurmi/Shinkafa a majalisar wakilai, ya shaida wa sashen Hausa na BBC a ranar Talata cewa, ‘yan bindigar sun kuma kashe jami’an ‘yan sanda biyu da fararen hula uku a yayin harin.

Akwai sama da fursunoni 400 a Kano da babu bayanai kan laifukan da suka aikata  —CP

Dan majalisar ya ce mai yiyuwa ne an yi garkuwa da mutane sama da 500 a kauyukan da lamarin ya auku. Ya ce hare-haren ya tilasta wa da yawa daga cikin mazauna garin barin gidajensu.

Advertisement

Ya kara da cewa wadanda suka ki arcewa daga garin na fama da matsin ƴan bindiga dare da rana, su kawo musu hari su na wulaƙanta su.

A kauyen Kanwa a ranar Asabar, ‘yan bindigan sun kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu mutane sama da 30. A Gidan Shaho da ke unguwar Nasarawa a ranar Litinin sun kashe ‘yan sanda biyu tare da raunata mutane da dama. Yanzu muna kokarin gano adadin mutanen da suka bata bayan harin (na baya-bayan nan),” in ji dan majalisar.

Advertisement

” Maganar gaskiya ita ce jami’an tsaron da aka tura jihar Zamfara sun gaji. Wasu daga cikinsu da aka tura a yankunan sun yi zarce tsawon lokacin da ya kamata su zauna a can da yawa saga cikin su sun kai kusan shekaru 10 a Zamfara. Sun daɗe fiye da yadda ya kamata, suna buƙatar a canja su. Mun kai rahoton wannan batu ga hukumomin da abin ya shafa amma ba su ce mana komai ba.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending