News
Majalisar Dokokin Jihar Kano Za Ta Yi Wa Dokar Masaratu Gyaran Fuska
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Majalisar Dokokin Kano ta amince da bukatar yin gyaran fuska ga dokar masarautu da nadin sarakuna ta jihar.
Shugaban Masu Rinjayen majalisar kuma mai wakiltar Mazabar Dala, Hussien Dala, ne ya gabatar da kuudrin a ranar Talata, ya kuma samu amincewan takwarorinsa.
Wani Mutum Mai Makarantar Sakandare Ya Karbi Kudin Jarabawar WAEC Da NECO Na Dalibai Ya Tsere Turai
An dai jima magoya bayan siyasar Kwankwasiyya suna kiraye-kirayen dawo da Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II kan kujerarsa da gwamnatin jihar da ta gabata ta Abdullahi Ganduje ta sauke daga kujerar Sarkin Kano.
Masu kiraye-kirayen na kuma neman ganin an soke sabbin masaraut Bichi, Gaya, Rano da kuma Karaye da ta kirkiro.
A daya bangaren kuma akwai masu adawa da soke sabbin masarautun.
Wasu dai na fargabar gyaran fuska ga dokar masarautun zai kai ga soke sabbin masarautun da aka nada ko rage wa sarakunansu daraja.
