News
Wani Mutum Mai Makarantar Sakandare Ya Karbi Kudin Jarabawar WAEC Da NECO Na Dalibai Ya Tsere Turai
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wani mutum mai makarantar sakandare a Ibadan ya karbi kudin jarabawar WAEC da NECO na daliban bana ya yi tafiyarsa ƙasar waje.
Wannan lamarin ya faru ne a garin inda wata baiwar Allah mai suna Adejoke Lasisi ta wallafa a shafinta cewa mai makarantar da ba ta son bayyana sunanta ya tsere da kudin daliban da suke kokarin rubuta jarabawar gama sakandare bana.
Wani Mutum Mai Makarantar Sakandare Ya Karbi Kudin Jarabawar WAEC Da NECO Na Daliba Ya Tafi Turai
Ta kara da cewa, har wa yau kafin tafiyar tasa ya sayar da gidansa da duk wata kadararsa da za ta kawo kudi.
Advertisements
