Connect with us

News

Kotu Ta Umurci Aminu Ado Bayero Da Ya Daina Ayyana Kansa A Matsayin Sarkin Kano

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Kotu a jihar Kano ta umurci Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da ya daina ayyana kansa a matsayin Sarki ta kuma umurci jami’an tsaro da su fitar da shi daga gidan sarauta na Nasarawa.

Advertisement

SolaceBase ta ruwaito cewa kotun karkashin jagorancin mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta ba da umarnin a ranar Litinin, 27 ga Mayu, 2024.

Majalisar dokokin Benue ta soke dokar biyan fansho na tsawon Rayuwa ga tsaffin Gwamnonin Jihar

Idan dai za a iya tunawa dai wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano karkashin jagorancin mai shari’a A.M Liman ta bayar da umarnin dakatar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano a ranar Alhamis din da ta gabata ta kuma dokar kafa masarautu biyar da aka rusa a jihar.

Advertisement

Hakazalika, umarnin ya hana Alhaji Nasiru Ado Bayero, Dr. Ibrahim Abubakar II, Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa da Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya su gabatar da kansu a matsayin sarakunan Bichi, Gaya Rano da Karaye.

Wadanda ake tuhumar sun hada da Alhaji Nasiru Ado Bayero, Dr. Ibrahim Abubakar II, Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa,  Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya, Sufeto Janar na ‘yan sanda, daraktan ma’aikatar tsaro ta kasa, jami’an tsaron farin kaya da Civil Defence da kuma rundunar sojojin Najeriya.

Advertisement

Yayin da masu karar suka hada da Babban Lauyan Jihar Kano, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending