News
Yanzu Yanzu: Majalisar Dattawa ta kira Sanata Abdul Ningi bayan dakatar da shi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Majalisar dattijai ta yi afuwa tare da kiran Sanata Abdul Ahmed Ningi da aka dakatar a ranar 12 ga watan Maris, 2024, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya rawaito.
An fara kiran ne bayan wani kudiri da mataimakin shugaban marasa rinjaye Sanata Abba Moro ya gabatar, wanda ya nuna nadama a madadin Sanatan da aka dakatar.
Shugaba Tinubu Zai Gabatar Da Jawabi A Zaman Hadin Gwiwa Na Majalisar Dokokin Kasar A Gobe Labara
Sanata Abba Moro ya yi alkawarin daukar cikakken alhakin abin da Ningi ya aikata, tare da amincewa da tsananin dakatarwar.
Halin da Sanatan ya yi a lokacin dakatarwar ya kasance abin dubawa da muhawara a cikin majalisar.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya jaddada basirar sanatan tare da bayyana shi a matsayin dan majalisar dattijai mai kima, inda ya kara da cewa matakin kiran Sanata Ningi ya wuce rarrabuwar kawuna na addini da kabilanci.
-
News3 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News3 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News4 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
