News
Majalisar Dattawa ta fara bincike kan kisan ‘yan Nijeriya 250 a kasar Habasha
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Majalisar Dattijai ta matsa ƙaimi domin gudanar da bincike kan kashe-kashe da ɗaure ‘yan Nijeriya sama da 250 a ƙasar Habasha.
Hakan ya biyo bayan wani ƙudiri mai taken, ‘Akwai buƙatar a gaggauta bincike kan kashe-kashen da aka yi wa ‘yan Nijeriya sama da 250 a ƙasar Habasha ba bisa ƙa’ida ba.
An kama mutum 29 da makamai da kayan maye lokacin Takutaha a Kano
Wanda shugaban marasa rinjaye, Sanata Simon Mwadkwon, ɗan Jam’iyyar Peoples Democratic Party, (PDP) mai wakiltar Filato ta Arewa, da Sanata Victor suka ɗauki nauyi.
Da yake gabatar da ƙudirin, Mwadkwon ya buƙaci majalisar dattijai da ta umurci kwamitocin ƙasashen waje da su haɗa kai da gwamnatin tarayya domin kafa kwamitin gaggawa da zai ziyarci jamhuriyar Habasha da nufin binciken abubuwan da ke faruwa ga ‘yan Nijeriya a ƙasashen ƙetare.
Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta umurtar ofishin jakadancin ƙasar Habasha da ya haɗa kai da tawagar kwamitocin majalisar dattawa kan ƙasashen waje domin samar da dawwamammiyar mafita kan matsalolin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.
Mwadkwon ya ce, “bidiyon da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na yanar gizo ya nuna cewa ‘yan Nijeriya na tsare a gidan yari mafi girma na ƙasar Habasha kuma suna cikin haɗari mai tsanani wanda ya buƙaci a gaggauta shiga tsakani da kuma yin cikakken bincike kan munanan ayyukan.”
Ya koka da cewa hakan na faruwa duk da kiraye-kirayen haɗin kai tsakanin ƙasashen duniya.
A wani labarin kuma An kama mutum 29 da makamai da kayan maye lokacin Takutaha a Kano
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
