Connect with us

News

An kama mutum 29 da makamai da kayan maye lokacin Takutaha a Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta ce ta kama mutum 29 ɗauke da makamai da kayan maye a lokacin bikin Maulidi na Takutaha da aka yi a fadin birnin ranar Alhamis.

A wani sakon bidiyo da mai magana da yawun rundunar Abdullahi Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce ana zargin waɗanda aka kama da yunƙurin tayar da zaune tsaye.

Advertisement

Matsalolin da ke janyo rufe gidajen mai a Najeriya

“Tun da farko gabanin hidimomin Maulidi Kwamishinan ƴan sanda na Jihar Kano CP Usaini Gumel ya ja hankalin al’umma da cewa su bi doka da oda a lokacin cewa duk wanda ya san zai fito don ta da hankalin al’umma to kuwa an baza jami’an tsaro don yin kame,” in ji ASP Kiyawa.

 

Advertisement

Rundunar ƴan sandan ta Jihar Kano na yawan yin holen mutanen da take kamawa bisa zarginsu da aikata miyagun laifuka kamar ƙwace wayoyi da dabanci da shaye-shaye da sauran su.

 

Advertisement

Kuma ana yawan samun tashe-tashen hankula a lokutan bukukuwan al’ada da na addini, inda masu son tayar da zaune tsaye ke amfani da damar don cutar da mutane.

 

Advertisement

Rundunar ƴan sandan ta ce ta kama mutum 29 ɗin ne a lokacin Takutahar a wurare daban-daban ne a fadin jihar, kuma suna ɗauke da muggan makamai da kayan maye.

 

Advertisement

A bidiyon da Kiyawa ke bayani an ga makaman da rundunar ta baje a gaban wadanda aka kama din a hedikwatar ƴan sanda da ke Bompai.

 

Advertisement

“Makaman da aka kama su da su sun haɗa da wuƙaƙe da almakashi da ɗan bida da adduna da wiwi,” in ji Kiyawa.

 

Advertisement

Rundunar ƴan sandan ta sa wasu daga cikin mutanen, wadanda dukkansu matasa ne ƴan tsakanin shekaru 18 zuwa 25, sun yi bayani kan yadda aka kama su da kuma irin makaman da suke riƙe da su.

 

Advertisement

“A yanzu haka mutanen suna babban sashen binciken manyan laifuka don yin bincike, sannan a gurfanar da su a gaban kotu,” a cewar mai magana da yawun ƴan sandan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending