News
Wani Makeken Rami Ya Rufta Da Akalla Mutane 50 A Kauyen Farin Doki
DAGA MUHAMMAD BASHIR MUSA
Rahotanni daga kauyen farin Doki dake yankin Erana a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja na nuna cewa, wani makeken rami da masu hakar zinari ke tona wa ya rufta da mutane akalla 50.
Tsohon Shugaban karamar hukumar Shiroro ASP Abdullahi Yarima Mai ritaya wanda lamarin ya faru a gaban idanunsa ya ce bayan kwashe sa’o’i biyar da ruftawar ramin an samu zakulo mutane shida da ransu sai dai suna cikin wani mawuyacin hali.
Wata Sabuwa: Har Yanzu Muna Yajin Aiki Har Sai An Samu Sanarwa – Ƙungiyoyin Kwadago
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja Abdullahi Baba Arah ya tabbatar wa Muryar Amurka da aukuwar lamarin, kuma ya ce jami’ansu na shirin zuwa wurin domin kai dauki, kuma suna cike da fatan samun wasu da dama, da kuma ransu.
Dama dai gwamnatin jihar Nejan ta haramta tona ma’adanan karkashin kasa ba akan ka’ida ba a jihar musamman a yankunan da kananan hukumomin ke fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
