News
Hukumar Kula Da Aikin ‘Yan Sanda Ta Saki Jerin Sunayen Kuratan Ƴan Sanda Dubu 10,000 Da Aka Ɗauka Aiki
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Hukumar kula da aikin ‘yan sanda (PSC) ta sanar da amincewa tare da fitar da jerin sunayen kuratan ƴan sanda dubu 10,000 da suka yi nasarar daukar su aiki a cikin ƴan sandan Najeriya.
PSC ta ce wadanda suka yi nasara an zaɓo su ne a cikin ƙananan hukumomi 774 na kasar.
A cewar hukumar an fitar da jerin sunayen ne bayan tsauraran matakai domin tabbatar da gaskiya da adalci.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, shugaban hulɗa da jama’a na PSC, Ikechukwu Ani, ya ce, “Hukumar ‘yan sanda ta amince tare da fitar da jerin sunayen mutane 10,000 da suka yi nasarar daukar su aiki a matsayin jami’in ‘yan sandan Najeriya.
“An amince da ɗaukar guda dubu 9,000 don daukar su a bangaren aiki na gaba ɗaya, yayin da dubu 1,000 aka dauke su a matakin ƙwararru.”
Ani ya bayyana cewa hukumar ta yi aiki tare da jagora daga masu ruwa da tsaki da suka hada da rundunar ‘yan sandan Najeriya, majalisar dokokin kasa, da kuma hukumar kula da dabi’u ta tarayya, domin tabbatar da daidaito wajen yaduwar waɗanda suka yi nasara a kananan hukumomi 774 na kasar nan.
Shugaban Hukumar Dokta Solomon Arase ya ce, “Na cike da kwarin guiwa domin wadannan matasa maza da mata suna wakiltar makomar tsaron kasarmu, kuma hakki ne na hadin gwiwarmu mu tabbatar da cewa tafiyar tasu ta fara kan rikon amana.
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News7 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News4 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
