Connect with us

News

Kaduna: Wata Amarya Ta Guntulewa Mijinta Mazakuta Yana Tsaka Da Bacci.

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Rahotanni Daga Jihar Kaduna na nuni da cewar wata sabuwar Amarya mai suna Habiba ta gutsurewa Angon ta mai suna Salisu Idris mazakuta  lokaci yana tsaka da bacci.

Advertisement

Daily Post ta ruwaito cewa Amaryar ta gutsurewa Angon nata mazakuta, mai kimanin shekaru 40 a sanyin subahi lokacin yana huce gajiya.

Sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya ya damu kan zargin karin girman wasu jami’ai ba bisa ka’ida ba

Bakin labarin ya faru a karamar hukumar Kudan ta Jihar Kaduna a ranar 26 ga watan Mayun daya gabata.

Advertisement

Salisu Idris ya ce ya kasa gane dalilin ta na yin haka saboda Auren soyayya suka yi watanni hudu da suka gabata, babu gaira babu dalili na dawo daga Masallacin Sallar subahi Ina kwance kawai ta Haye mun ruwanci da kakkaifar wuka ta hari mazakuta na saura kadan ta gutsure ta duka sai da makota suka kawo mun dauki; inji shi

Da farko an fara garzayawa da Salisu Idris, zuwa Asibiti dake Kudan daga nan aka mayar da shi babban Asibitin Karamar hukumar Makarfi, sai dai yanzu matsalar ta Saka Kazanta har an wuce da shi babban Asibitin Shika.

Advertisement

Zuwa yanzu jami’an Yan sanda sun yi nasarar tattarata suna gudanar da bincike da zarar an kammala zaa mikata gaban kuliya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending