Connect with us

News

Kwankwaso Ya Maka Hukumar EFCC A  Kotu

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD YASIR 

 

Advertisement

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya maka hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC a kotu, Inda ya nemi kotun ta hana hukumar ta kama shi.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa an gabatar da karar ne a babbar kotun Kano a gaban mai shari’a Yusuf Ubale.

Advertisement

A Ƙarshe Dai Jaruma Mansura Isa Ta Sake Ɗaura Aure

Hukumar ta EFCC ta fara bincike kan zargin da ake yiwa Kwankwaso na almundahanar wasu kudade

Wata majiya mai tushe ta ce a karar Kwankwaso na  bukatar kotun ta hana hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC tsare shi.

Advertisement

Idan dai za a iya tunawa Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Hukumar EFCC ta fara bincike kan zargin karkatar da kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe da jam’iyyar NNPP ta yi a zaben 2023. Binciken dai ya mayar da hankali ne kan zarge-zargen da ake yi wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da tawagarsa, musamman gazawar kwamitin ayyuka na jam’iyyar a ƙarƙashin jagorancin Kwankwaso, wajen biyan wakilan jam’iyyar da suka yi aiki a lokacin zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna.

EFCC na bin diddigin ikirarin da Kwankwaso da sakatariyarsa, Misis Folashade Aliu, suka yi na karkatar da kuɗaɗen ta hanyar wani asusun kamfen na sirri da kuma bayar da tallafi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending