Connect with us

News

Likitoci A Asibitocin Gwamnati Za Su Fara Yajin Aikin Makwanni Biyu A Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kungiyar likitocin hakori ta kasa (NAGGMDP) reshen Kano ta bayyana shirin fara yajin aikin gargadi na tsawon mako biyu domin nuna rashin amincewa da wasu matsaloli da suka dabaibaye tsarin kiwon lafiyar jihar.

Advertisement

A cikin sanarwar da shugaban kungiyar, Dr Aminu Kabir Muhammad ya sanya wa hannu a ranar Laraba, kungiyar ta bayyana cewa za a fara yajin aikin a asibitoci fadin jihar daga karfe 12:00 na safe ranar 17 ga watan Yuni 2024.

Kwankwaso Ya Maka Hukumar EFCC A  Kotu

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa sanarwar ta bayyana takaicin likitocin na rashin biyan albashi, rashin yanayin aiki, da rashin tsaro.

Advertisement

A cewar sanarwar jami’an lafiya 61 na bin  gwamnatin jihar Kano  albashin watanni biyu. Bugu da ƙari, likitocin suna kokawa da rashin isassun kayan aiki da kayayyakin more rayuwa a asibitoci, wanda ke hana su bada kulawa mai inganci.

”Rikicin wurin aiki wani babban abin damuwa ne ga NAGGMDP. Sanarwar ta ba da rahoton hare-haren da jama’a da jami’an tsaron gwamnati suka kai kan kwararrun likitocin.

Advertisement

 

Kungiyar ta ce ta yi yunkurin magance wadannan matsaloli da gwamnati amma ba ta ga wani ci gaba ba. Sakamakon haka ‘ya’yan kungiyar NAGGMDP sun kada kuri’ar tsunduma yajin aikin gargadi na mako biyu daga ranar 17 ga watan Yuni idan ba a biya musu bukatunsu ba.

Advertisement

Barazanar yajin aikin na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar Kano ke fuskantar kalubale na samun ingantaccen kiwon lafiya.

NAGGMDP na fatan dakatar da aiki zai tilastawa gwamnati daukar mataki tare da inganta yanayin aiki ga likitocin jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending