News
Taken Najeriya ba zai magane matsalar Najeriya ba – Sanata Shehu Sani Ga Shugaba Tinubu
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Sanata Shehu sani ya isar da sakon yan Najeriya a wajen liyafar cin abinci na ranar Demokradiyya da Shugaba kasa Bola Ahmad Tinubu ya gayyace shi.
Da farko sanata Shehu sani ya fara da sanar da Shugaba Tinubu halin da Najeriya ke ciki na Tsadar rayuwa.
Har Yanzu Bamu Cimma Matsaya Ba Kan Mafi Karancin Albashi Ba – Kungiyar Kwadago
Shehu Sani ya kara da cewa ya kai shugaban kasar Najeriya ka sani da cewa, “taken Najeriya ba zai gyara ƙasa ba, gaskiya da rikon amana da kyawawan jagoranci shike gyara Najeriya.
Sanata sani ya bayyana cewa, ” Akwai matasa da yawa a Najeriya masu gabatar da zanga-zangar neman yanci a Najeriya, ya kamata a basu dama wajen gabatar da zanga-zangar lumana don tabbatar da sahihiyar Demokradiyya ta yanci a Najeriya.
Sanatan ya bayyana haka ne a wajen liyar cin abinci da a gabatar a Abuja wanda matar shugaban kasa Oluremi Tinubu ta shirya.
-
News3 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
