News
Har Yanzu Bamu Cimma Matsaya Ba Kan Mafi Karancin Albashi Ba – Kungiyar Kwadago
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyoyin Kwadago sun yi watsi da ikirarin shugaban kasa Bola Tinubu na cewa an cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashi.
Jaridar Punch ta ruwaito shugaba Tinubu ya yi ikirarin cewa an cimma matsayar ne kan batun sabon mafi karancin albashin da aka dade ana ja-in-ja tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin kwadago a kasar.
Hukumar NRC Ta Bayyana Lokacin Da Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Kano Zai Fara Aiki
A jawabinsa na bikin ranar dimokuradiyya a wannan shekarar ta 2024 da ya gudana a Abuja ranar Laraba, Tinubu ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a aika da wani kudirin doka ga majalisar dokokin kasar domin ta amince da mafi karancin albashi.
Shugaban ya jaddada cewa gwamnatinsa ta zabi tsarin dimokuradiyya wajen magance bukatun kungiyoyin kwadago a kasar.
-
News3 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
