News
Hukumar NiMet Ta Yi Hasashen Samu Tsawa Da Ruwan Sama Na Kwanaki 3 A Wasu Sassan Jihohin Najeriya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen yanayin tsawa da ruwan sama daga ranar Lahadi zuwa Talata a fadin kasar.
Hasashen yanayi na NiMet da aka fitar ranar Asabar a Abuja ya yi hasashen tsawa da za a yi ranar Lahadi a wasu sassan jihohin kasar nan kamar Gombe, Bauchi, Borno, Adamawa, Jigawa, Taraba da Kaduna.
Kotu Ra Ɗaure Matashi Shekara 1 A Gidan Gyaran Hali Kan Satar Kayan Abincin 1,000
Haka zalika Ta yi hasashen tsawa a sassan jihohin Zamfara, Kebbi, Kano, Borno, Adamawa Bauchi, Katsina, Kaduna, Jigawa, Yobe, da Taraba da yammacin ranar.
“An yi hasashen tsawa a wasu sassan jihohin tsakiyar kasar kamar; Plateau, Nasarawa, Babban Birnin Tarayya, Jihohin Binuwai da Neja a safiya.
“Bayan da rana, akwai yiwuwar tsawa a kan wasu sassan; Kogi, Niger, Plateau, Benue, Nasarawa da babban birnin tarayya Abuja
“Biranen kudancin kasar ana sa ran za a yi ruwan sama da safe musamman sassan Imo, Ogun, Ondo, Delta, Edo, Cross River, Bayelsa da Legas.
Hukumar ta yi hasashen za a yi tsawa da ruwan sama a sassan jihohin Ogun, Ondo, Edo, Delta, Imo, Ebonyi, Cross River, Rivers, Akwa Ibom, Bayelsa, da Legas da rana da kuma sa’o’i na yamma.
A cewar NiMet, ana sa ran za a yi hadari sanyin safiyar ranar Litinin a sassan jihohin Yobe, Borno, Adamawa, Bauchi, Gombe, Kano, Jigawa, Taraba da Kaduna.
“Yayin da maraice da yiwuwar tsawa a sassan jihohin Taraba, Adamawa, Zamfara, Jigawa, Sokoto, Kebbi, Kano, Bauchi da Kaduna.
“Da sanyin safiya ana sa ran za a yi tsawa a wasu sassan Filato, babban birnin tarayya da kuma jihar Nasarawa .
Hukumar NiMet ta yi hasashen tsawa a safiyar ranar Talata a wasu sassan jihohin Taraba, Adamawa, Katsina, Sokoto, Kebbi, Bauchi da Kaduna.
