News
Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci A Zamfara Sun Kashe Biyu Tare Da Yin Garkuwa Da Wasu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wasu ƴan bindiga suka kai hari wani masallaci a ƙauyen Tazame da ke ƙaramar Bungudu a Jihar Zamfara.
Channels tv ta ruwaito cewa an kai harin ne a lokacin da mutane ke ƙoƙarin gudanar da sallar asuba yayinda ƴan bindigar suka buɗe wuta wa masallata inda suka kashe Ladanin masallacin da ɗan uwansa tare da raunata Limamin a safiyar ranar talata.
KANO: Kotu ta daure mutumin da ya ke turawa matar aure fina-finan batsa ta WhatsApp.
Baya ga haka ne, sun kuma yi garkuwa da wasu da dama daga cikin masallatan.
A ƴan kwanakinnan, ƴan bindiga sun kai hare-hare da dama wa masallatai da yin fashi a shaguna gami da garkuwa da mutane.
Rundunar Ƴan sandan Jihar ta aika da ƙarin jami’anta yankin don ganin an inganta tsaro tare da ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, kamar yadda kakakin Rundunar, ASP Yazid Abubakar ya fada.
-
Opinion6 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion6 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
