News
Gwamatin Tarraya Ta Ware Naira Biliyan 155 Don Raba Abinci Ga Magidanta Da Bai Wa Kowannen Su Dubu 50
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da shirin gina ƙasa da tallafawa magidanta a yayin wani zama da Majilisar kula da harkokin tattalin arziƙin ƙasa, NEC a Abuja.
Wani jawabi da ya fito daga ofishin mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya ce manufar shirin su ne dan a inganta harkokin noma da tattalin arziƙi gami da bada tallafi domin rage raɗaɗin talauci ga ƴan Najeriya.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Shirin wanda ya samu goyon bayan Majalisar ta NEC, ya ƙunshi rarraba kuɗaɗe da yin ayyukan more rayuwa a dukkan shiyyoyin ƙasarnan guda shida, inda za a bada tallafin naira dubu 50 ga iyalai 100,000 a kowace Jiha na tsawon watanni uku.
Ya ƙara da cewa gwamnatin ta ware naira biliyan 155 domin sayan kayan abinci da kuma raba su ga magidanta don samu sauki ta fuskar mallakar abinci a cikin al’umma.
Ngelale ya ce, shugaba Tinubu ya yi kira ga gwamnoni da su bada haɗin kai wajen ganin sun samar da buƙatun al’ummarsu da kuma inganta harkokin noma.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News7 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
