News
Mutum Aƙalla Shida Ne Suka Mutu Bayan Wata ‘Yar Ƙunar-baƙin-wake Ta Tashi Bam A Taron Biki
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Mutum aƙalla shida sun mutu bayan wata ‘yar ƙunar-baƙin-wake ta tashi bam da ke jikinta a ƙaramar hukumar Gwoza ta Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya ranar Asabar.
Kamfanin dillancin labaran News Agency of Nigeria (NAN), wanda ya ambato Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Borno Yusuf Lawal yana tabbatar da aukuwar lamarin, ya ƙara da cewa mutum kimanin 15 ne suka jikkata.
Ganau sun ce matar, wadda ke goye da jariri, ta tashi bam ɗin ne a wani wurin biki a Marrarraban Gwoza.
NAN ya ambato wani ganau mai suna Muhammed Kasim yana cewa “mun ji babbar ƙarar fashewar wani abu da kuma tashin ƙura; sannan muka ga gangar jikin mutane a ƙasar.”
Ya ce an garzaya da mutanen da suka jikkata asibitin da ke Gwoza domin yi musu magani.
‘Kisa a maƙabarta’
Kazalika bayanai sun nuna cewa wani ɗan ƙunar-baƙin-waken ya tayar da bam a maƙabarta lokacin da aka je binne mutanen da suka rasu a harin bam na farko.
Mutumin, wanda ya saje a cikin masu jana’iza, ya kashe mutum ɗaya tare da jikkata wasu.
Tuni dai rundunar sojojin Nijeriya da ke aiki a yankin ta sanya dokar hana fita a Gwoza.
