News
Fadan Daba : Babu Daga Kafa Duk Wanda Aka Samu Da Mugun Makami — Kwamishinan Yan Sanda
DAGA YAASIR SANI ABDULLAHI
Yanzu haka dai Kwamishinan Yan Sandan jihar Kano, CP Salman Dogo Garba ya bada umarnin duk wanda ya fito harkar daba da masu tsaya musu ayi maganinsu ba tare da wani bata lokaci ba.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da Kakakin ‘yan sandan jihar SP Haruna Kiyawa ya fitar.
Mutum Aƙalla Shida Ne Suka Mutu Bayan Wata ‘Yar Ƙunar-baƙin-wake Ta Tashi Bam A Taron Biki
Kiyawa yace “A saboda haka, duk wanda aiki ya biyo ta kansa ba daga kafa. An bawa Yan Sanda kayan aiki domin kare lafiya da dukiyoyin al’umma ina fatan al’ummar jihar Kano zaku bamu hadin kai.
“Yanzu haka, ana ta farautarsu duk wasu masu aikata munanan ayyuka da laifuka a fadin jihar.
“Duk mutumin da aka samu muggan makamai kamar Fate Fate, ‘Switzerland’, Dan Bida, Gariyo, a gidansa shima za a kamashi.
Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa Wannan dai na zuwa ne bayan da fadan daba yayi kamari a cikin tsohon birnin na Kano inda wasu ‘yan daba suke tayar da hankalin jama’a babu gaira ba sabar.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News4 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
