Connect with us

News

Wani Jirgin Saman Sojin Najeriya Ya Yi Hatsari A Jihar Kaduna.

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Wani jirgin sama na sojin Najeriya ya yi hatsari a kauyen Tami da ke yankin Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Wani mazaunin yankin ya ce jirgin sojin mai saukar ungulu ne, kuma ya yi hatsari ne da misalin karfe 5 na asubar Litinin din nan.

Ka Guji Maimaita Kuskuren Da Buhari Ya yi Na Son Zuciya  – Shehu Sani Ya  Gargadi Tinubu

Mazauna yankin sun bayyana cewa matukin ya fito daga cikin tarkacen jirgin da ya fado.

Bayan nan sojoji suka yi gaggawar zuwa suka yi wa yankin kawanya tare da fara bincike.

Sojojin sun kuma hana mutane isa wurin da tarkacen jirgin yake.

Advertisement

An ce jirgin yana tsaka da aikin sintiri a yankin ne ya samu matsala, lamarin da ya haddasa faduwarsa.

Kawo yanzu Hedikwatar Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ba ta fitar da sanarwar game da lamarin ba.

Kakakin rundunar a Jihar Kaduna, Alaere Eyinimiere Obidake, ya ki daga kiran da muka yi masa domin neman bahasi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending