Connect with us

News

Yawan bashi : KEDCO Ta Yankewa Jami’ar aliko Dangote wutar lantarki

Published

on

DAGA KABIR BASIRU FULATAN

 

 

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano da Jigawa da Katsina (KEDCO) ya katse wutan lantarki na Jami’ar Aliko Dangote da ke Wudil, saboda basussukan da ake binta da ya kai har Naira miliyan ₦248m.

 

Alhaji Abubakar Yusuf, Manajan Daraktan KEDCO ne ya bayyana haka a wata tattaunawa ta wayar tarho da Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, NAN a yau Litinin, inda yace Naira miliyan ₦20m ne kacal jami’ar ta iya biya a cikin bashin.

Advertisement

Yusuf ya bayyana cewa KEDCO ba ta da wata mafita illa ɗaukar wannan tsattsauran mataki, inda ya jaddada mahimmancin jami’ar na biya kuɗin da ya kamata kafin a dawo da wutar lantarki.

Ya nanata matsayin kamfanin na cewa ba tare da biyan kudi ba, jami’ar za ta ci gaba da zama cikin duhu.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending