News
Rikicin daba: Mazauna unguwar Dorayi sun koka kan kin auren ‘ya’yansu mata da samari keyi
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Mazauna yankin Dorayi da ke karamar hukumar Gwale a jihar Kano, sun koka da yadda matsalar ‘yan daba ta yi kamari a yankin inda ya sa samari ke kin auren ‘ya’yansu mata.
Jaridar Nigerian tracker ta rawaito An tabo wannan batune a yayin wani taron masu ruwa da tsaki na al’umma da nufin magance matsalar ‘yan daba a yankin da kuma makwabta. unguwannin
Taron wanda ya samu halartar dimbin jama’a daga wakilan yankunan da abin ya shafa, da suka hada da unguwar Dorayi Karama, Chiranci, Gidan Dakali, Ja’en Makera, Gobirawa, da Kan Fako, kungiyar raya al’ummar Dorayi Youths ce ta shirya
Da farko dai kungiyar ta gana da ‘yan kasuwar da abin ya shafa wadanda suka yi asara mai yawa a rikicin baya-bayan nan da ya yi sanadiyar rayuka da dama ciki har da kwamandan ‘yan banga.
Kungiyar ta kuma hada kai da iyaye da matasa domin inganta zaman lafiya.
Malam Muhammad Tijjani, shugaban kwamitin tsaro na Dorayi, ya bayyana cewa sun tattauna sosai kan matsalar tsaro tare da samar da tsarin da za a magance shi.
Tijjani ya nuna damuwarsa kan yadda yace mafi yawan ‘yan daba da ke ta’addancin matasa ne ‘yan kasa da shekaru 35
Irin wadannan matasan su yakamata su Zama jakadu na kwarai domin ganin a Sami cigaba Mai dorewa Kuma rashin Hakan sai su haifar da matsala. A cewar sa
daga karshedai Ya yi nuni da cewa, masu hannu da shuni a yanzu suma suna sha,awar aurar da ‘ya’yansu mata
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
