Connect with us

News

Kotu Ta Yanke Wa Wani Mahaifi Hukuncin Zaman Kurkuku Na Tsawon Shekaru 17 Bisa Laifin Yi Wa ‘Yarsa Fyade

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Kotu dake Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa ta yanke wa wani mahaifi mai shekara 41 Baridapsi Needem hukuncin zama a kurkuku na tsawon shekaru 17 bayan an kama shi da laifin yi wa ‘yar cikinsa mai shekaru 14 fyade da yi mata ciki.

Advertisement

Yarinyar ta haifi ‘ya mace kafin kotu ta yanke wa mahaifin hukunci.

Hukumar NDLEA  Za Ta Fara Yiwa Ma’aurata Gwajin Ƙwaya Kafin Aure A Kano

Kungiya mai zaman kanta ‘Gender Response Initiative Team’ ta ce ta samu labarin abin da Needem ke aikatawa da ‘yarsa daga wajen wata makwabciyar su inda a lokacin yarinyar na da cikin wata biyar.

Advertisement

Kungiyar ta ce makwabciyar ta ce Needem ya rabu da matarsa wato mahaifiyar ƴarsa da tun bayan rabuwarsu ya maida ita matarsa.

“Mahaifin ya fara yi wa ‘yarsa fyade a shekarar 2020 inda a lokacin yatsun sa ne yake sakawa a gaban yarinyar sannan a 2022 ya rika danne ta har sai da ya ɗirka mata ciki.

Advertisement

A kotun lauyan da ya shigar da karar Pere Egbuson ya ce Needem ya fara yi wa ‘yar sa fyade tun tana shekara 7.

Egbuson ya gabatar da sakamakon gwajin DNA wanda ya tabbatar cewa Needem shine mahaifin jaririyar da ƴarsa ta haifa.

Advertisement

Alkalin kotun D.E. Adokeme ta yanke wa Needem hukuncin zama a kurkuku na shekara 17.

 

Advertisement

Premium Times

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending