News
Firgici Ya Kunno Kai A Rano Da Ke Kano Bayan Da Wasu Masu Kama Da ‘Yan Daba Suka Mamaye Fadar Masarauta
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Firgici ya kunno kai a Rano da ke Kano bayan da wasu masu kama da ‘yan daba suka mamaye fadar masarauta.
A cikin wata wasika da aka rubuta wa kwamishinan ‘yan sandan jihar kame yanda jaridar SolaceBase ta rawaito cewa ‘yan dabar sun yi sansani a fadar Sarkin Rano tun a ranar Lahadi da wasu da ba a tantance ko suwaye ba.
Ta ce har yanzu ba a san dalilan wadannan mutane masu dauke makamai ba, ana daukar zaman nasu a matsayin barazana ga tsaron rayuka da dukiyoyi al’ummar yankin.
A cewar wasikar, mazauna masarautar Rano mutane ne masu zaman lafiya da kullum suna gudanar da harkokinsu ba tare da haifar da tarzoma ba.
Ta ce a tsawon shekaru masarautar Rano ta samu zaman lafiya ba tare da wata matsala ba kuma hukumomin tsaro na iya shaida wannan tarihin da masarautar ke da shi.
-
News3 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
