News
Hajj 2024: Majalisar Tarayya Ta Kafa Kwamitin Binciken Hukumar NAHCON Bisa Zargin Tafka ‘Badakala
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya kafa wani kwamiti na musamman da zai binciki Hukumar Alhazai ta ƙasa, NAHCON da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Abuja, bisa zargin kin baiwa mahajjata kulan da ya kamata a lokacin aikin Hajji na bana.
Tajudeen ya sanar da kwamitin mutum tara, karkashin jagorancin Sada Soli (APC, Katsina), don gudanar da binciken yayin zaman majalisar na ranar Alhamis.
Zango Ɗaya Tak Shugaba Tinubu Zai Yi, Shima Uba Sani Ta Shi Ta Ƙare A Kaduna E—l-Rufai
Kafa kwamitin ya biyo bayan amincewa da kudirin da Umar Bio (APC, Kwara) ya gabatar.
Kudurin dai mai taken: Bukatar gaggawa ta binciki Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta FCTA, kan rashin samar da isasshen kula ga Alhazai a lokacin aikin Hajjin bana.
Da yake gabatar da kudirin, Bio ya zargi NAHCON da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta FCTA da rashin tabuka komai duk da miliyoyin da alhazai suka biya da kuma tallafin Naira biliyan 90 da gwamnatin tarayya ta bayar.
Ya yi gargadin cewa idan ba a dauki matakan gaggawa ba, NAHCON za ta iya ci gaba da yin irin haka tana azabtar da alhazai a lokacin aikin Hajji.
Shima Ali Isa daga jihar Gombe ya bayyana cewa an rataya wa NAHCON nauyi masu yawa da yafi ƙarfinta. ” Ya kamata a sauke mata wasu nauyin da aka ɗora mata, in ba haka ba, za a rika samun matsaloli ne kawai kuma Alhazai su yi ta wahala, bayan sun biya maƙudan kudade.
Bayan sauraren wannan kudiri, kakakin majalisar Abbas, ya naɗa kwamitin musamman domin binciken abin da ya gudana a lokacin aikin Hajjin.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
