Connect with us

News

Wasu Ma’aurata Sun Fada Komar  Jami’an Yan  Sanda Bisa Yunkurin Sayar Da ‘Dan Su

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Ma’aurata sun shiga hannun ‘yan sanda yayin da suke kokarin sayar da jaririnsu mai shekaru biyu don su yi ƙaura zuwa ƙasar waje.

Wani mutum mai shekaru 28, Uchenna Eziekwe, da matarsa, Chineye, sun shiga hannun ‘yan sanda a Lagos bisa zargin yunkurin sayar da jaririnsu mai shekaru biyu.

Shugaba Tinubu Ya Cire Surukin Buhari Daga Shugabancin Kamfanin Buga Kuɗi Da Muhimman Takardun Sirri

A cewar ‘yan sanda, ma’auratan sun yi niyyar amfani da kudin da suka samu daga sayar da jaririn domin yin ƙaura zuwa kasar Kanada, inda suka yi fatan samun rayuwa mai kyau.

An kama su ne da ‘yan sanda daga Ofishin ‘Yan Sanda na Isolo bayan da aka basu bayanai daga shugabannin Asibitin Janar na Isolo.

Uchenna da matarsa sun bayyana niyyarsu na sayar da ɗansu namiji a Asibitin Janar na Isolo, a yankin Isolo na jihar.

Advertisement

An samu labari cewa shugabannin asibitin sun sanar da ‘yan sanda na sashen Isolo bayan sun amince da bukatar ma’auratan.

Uchenna, yayin da yake magana da ‘yan jarida, ya ce, “Yanke shawara mai wahala ne, amma ba mu da wani zaɓi illa sayar da ɗanmu. Mun ji cewa zai fi alheri mu sayar da shi ga wanda zai kula da shi fiye da barinsa ya mutu da yunwa.”

Ya amince tare da shaida cewa, ra’ayin sa ne, da farko matarsa bata amince ba, sai da yasha wahalar shawo kan matar tasa. duk da cewa da kyar ta amince.

Kakakin ‘yan sanda na jihar Lagos, Benjamin Hundeyin, ya ce, “A ranar Talata, kusan ƙarfe 2:45 na rana, Ofishin yan sanda na Isolo ya samu bayanin cewa wasu ma’aurata sun je Asibitin Janar na Isolo suka bayyana niyyarsu na sayar da ɗansu namiji.”

Ya ƙara da cewa, “Bayan samun bayanin, jami’an sashen sun yi gaggawar zuwa asibitin, inda suka kama Uchenna Eziekwe, mai shekaru 28, da Chineye Eziekwe, mai shekaru 22, suna kokarin sayar da ɗansu mai shekaru 2 a duniya.

Bayan tambayoyi, ma’auratan sun bayyana cewa sun yanke shawarar sayar da jaririn ne domin ya samu damar tafiya zuwa Kanada don neman rayuwa mai kyau,” in ji Hundeyin.

Advertisement

 

 

 

 

WIKKI TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending