News
Stallion Times Ta Shirya Taron Tattaunawa Akan Shugabanci Na Gari A Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban Kamfanin Stallion Times Media Services, Isiyaku Ahmed, ya bayyana cewa shugabanci nagari ya kunshi hada kai da gwamnati da kungiyoyin fararen hula domin tabbatar da gaskiya da rikon amana.
Tattaunawar da ta kunshi kafafen yada labarai, kungiyoyin farar hula, gwamnati, da kuma kamfanoni masu zaman kansu na jihar Kano.
Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa an gudanar da taron ne a cibiyar ‘yan jarida da ke Kano a ranar Alhamis.
Ahmed ya lura da cewa yan Najeriya na fama da matsananciyar rashin aminta da gwamnati wajen aiwatar da manufofin da ke nuna muradin ‘yan kasa.
“Kyakkyawan shugabanci shi ne tsarin da ake sarrafa yan kasa da gudanar da ayyukanta, da kuma tsarin da ita da al’ummarta ke bi da su,” inji shi.
Makasudin tattaunawar da aka yi a kan shugabanci na gari, wanda gidauniyar MacArthur ta tallafa, shi ne wayar da kan masu gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu don inganta samar da ababen more rayuwa da muhimman ayyuka ga ‘yan kasa.
Tattaunawar ta zagayowar ta mayar da hankali ne kan inganta karfin masu ruwa da tsaki kan tsare-tsare da dabarun yin aiki mai inganci tare da kamfanoni masu zaman kansu, don karfafa gwiwar ‘yan kasa da su shiga harkokin mulki da inganta ayyukan more Rayuwa
