News
An Gano Gawar Mutane Uku A Binne Cikin Rami, A Gidan Wani Mai Siyar Da Kayan Kano
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Hukumomin tsaro a jihar Kano, sun Kama Wani mutum mai sana’ar siyar da kayan miya , bisa zarginsa da binne mutane a gidan sa dake garin Yarbarau, a Karamar hukumar Dawaki Kudu ta jihar.
Ana zargin mutumin da laifin yin garkuwa da mutane, idan ba a kawo kudin fansa ba, sai ya kashe su , ya binne a cikin gidan kamar yadda wasu daga cikin mazauna yankin Suka bayyana.
Ya Kamata A Ce Tun Farko Najeriya Ta Koyi Darasi Daga Zanga-zangar Da Ta Ɓarke A Ƙasar Kenya
Rahotanni na nuni da cewa an samu gawar mutane uku a gidan kuma tuni Suka Yi gangami tare da rushe gidan baki dayansa.
Wani matashi ya ce suna zarginsa da Laifin sace yan uwansa har wasu mutanen ,kuma bayan da Jami’an Tsaro Suka zo gudanar da bincike ne aka gano Wani rami dauke da mutane a cikin buhu.
Kazalika Wani Mazaunin garin Yarbarau , ya ce ji aka yi wari yana tashi a gidan shi yasa ma aka balle kofar gidan har ma’aikata Suka zo , har Suka gudanar da binciken gano gawarwakin mutanen.
Al’ummar yankin sun Yi Kira da a hukunta dukkan wadanda suke da hannu wajen aikata wannan rashin imani.
Sai dai mun Yi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar Yan Sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, amma abun ya ci tura.
