News
Sabon Mafi Karancin Albashi Buhun Shinkafa Kadai Za A Iya Saye Da Shi —Ndume
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Babu shakka Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu bai gama sukar Shugaba Bola Tinubu ba akan faɗar gaskiya.
Sukar da ya yi wa Shugaban ƙasa kwanan baya ne ya kai ga tsige shi daga mukamin Babban mai tsawatarwa na Majalisar Dattawan Najeriya.
Rundunar ‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 1,284 Da Ake Zargi Da Aikata Mabambanta Laifuka
Haka Ita ma Jam’iyyarsa ta APC ta buƙaci da ya fice ya koma Jam’iyyar adawa inda yafi so.
Dan Majalisar Dattawan dai ya amince da tsige shi da akayi bisa kyakkyawan fata, tare kuma da shan alwashin ba zai daina fadin gaskiya ga masu Mulki ba.
Yayin wata tattaunawa da ‘yan jarida, an nemi Ndume da ya yi tsokaci game da mafi karancin albashi na Naira 70,000, wanda Tinubu ya shawo kan kungiyoyin kwadago suka amince da shi.
“Jama’a na cikin wahala, mutane sun fusata, mutane ba su cikin walwala. Na ji dadi da Shugaban kasa tare da NLC suka amince da ƙara albashi zuwa Naira 70,000 wanda hakan abu ne mai kyau, amma fa ana buƙatar fiye da haka, domin a gaskiya kuɗin ba su wuce siyan buhun shinkafa ɗaya ba”.
“Don haka ina kira ga Shugaban ƙasa da ya bude kunnensa ya saurari Jama’a,” inji ɗan Majalisar.
Tun da farko ɗan Majalisar ya bayyana matakin da ya ɗauka a matsayin matakin masu kishin ƙasa, inda ya shawarci Shugaba Tinubu da ya saurari kukan ‘yan Najeriya, ya kuma yi gaggawar magance matsalar.
“Har ila yau, ya nanata cewa rashin kishin ƙasa ne a goyi bayan Shugaban kasa akan ko wane irin ƙuduri, kishin kasa ne kuma a fadi gaskiya ba ga Shugaban ƙasa kaɗai ba, har ma ga kowa a kan lamarin, har yanzu ina nan akan haka, kuma na san cewa Allah yana tare da mai fadin gaskiya ko da yaushe.
“Don haka na san cewa ban yi kuskure ba, jama’a ma ba su yi kuskure ba don sun fadi gaskiya da tsayawa kan gaskiya, kuma ina rokon da Shugaban ƙasa da nake sa ran sakon ya isa gare shi ya dubi abin da na fada, kuma a dauki matakan da suka dace domin magance wahalhalun da jama’a ke ciki”.
