News
Daga Yanzu Laifi Ne Biyan Ma’aikaci Albashin Kasa Da Naira Dubu 70 Ko Da Ƴan Aikin Gida Ne —Godswill Akpabio
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce duk ma’aikatan gwamnati da ma waɗanda ba na gwamnati ba irin su Masu gadi,Direbobi,Masu shara da wanke – wanke duk sun shiga sahun karɓar mafi ƙarancin albashin Naira 70,000.
Akpabio ya bayyana haka ne a zaman majalisar da aka yi a jiya Talata bayan da Majalisar ta amince da sabon kudirin biyan mafi karancin albashi ga ma’aikata.
Aliko Dangote Dan Kishin Kasa Ne Kuma Yana Kan Aikin Ceto Tattalin Arzikin Najeriya — DR Abbati Bako
Ya ce, “Idan kai tela ne kuma ka dauki ma’aikata to ka sani ba za ka biya su kasa da Naira 70,000 ba. Idan ke uwa ce mai jariri kuma kina son daukar yar aikin gida don kula da yaron, itama zaki biya ta daidai da mafi ƙarancin albashin da aka amince da shi , wannan doka Ya shafi kowa da kowa.
“Idan ka dauki direba ko mai gadi ba za ka biya su kasa da N70,000 ba. Don haka, na yi matukar farin ciki da aka ƙaddamar da haka , kuma a yanzu muna sa ran masu ɗaukan ma’aikata su inganta kan abin da aka kafa kowa ya bi.
”Haka kuma Ina taya Kungiyar Kwadago ta Najeriya, da ma ɗaukacin ƴan Nijeriya, da Majalisar Dokoki ta kasa murnar wannan doka da aka kafa, wanda har ma aka rage wa’adin tattaunawar daga shekaru biyar zuwa shekaru uku, duba da yadda ake tsadar rayuwa ke cigaba. Wannan kuma, wani muhimmin doka ne, don haka ina taya murna.”
