News
Sojoji sunja kunnan masu Shirin yin zanga zanga a Nigerian
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar Tsaron Najeriya ta ja Kunnan masu shirin yin zanga-zangar yaki da tsadar rayuwa a Najeriya ida ta ce rundunar ba zata kyale su tayar da fitina ba.
Hedikwatar Tsaron ta ja Kunnan cewa sojoji ba za su zura ido a yi kone-kone da dangoginsu na karya doka da oda da sunan zanga-zangar ba.
Sojojin sunce kundin tsarin milkin kasa ya bada dama al,umma sayi zanga zanga Kuma adan haka baice a tada tarzoma a gurin yin zanga zanga ba
Dubban ’yan Najeriya musamman matasa sun ayyana 1 ga watan Agusta da ke tafe a matsayin ranar fara zanga-zangar gama gari ta tsawon kwanaki 10 a fadin kasar kan tsadar rayuwa da ta addabi kasar.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
