News
Mutune 3 sun mutu har lahira sanadiyyar faduwar wani gani a Jahar Legos
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legos wato LASEMA a ranar alhamis ta tabbatar da mutuwar wasu ma,aikata mutun uku a wani gini daya ruftamusu a unguwar estate Arowojobe dake yankin Maryland ta jihar
Babban sakataren Hukumar DR Olufemi Oke -Osanyintolu ne ya tabbatar da faruwar hakan a wata sanarwa daya aikewa Kamfanin dinlanchin labarai na Nigerian ( NAN )
Yace lamarin ya faru ne a gida mai lamba 13 wilson Mba street Arowojobe Estate Maryland a jihar Legos
Yace an tabbatar da mutuwar mutun uku 3 ne a ginin ma,aikata dake wurin
Hukumar ta samu Kiran gaggawa game da wani gini daya ruguje a addireshin dake Sama ginin da misalin karfe 3 ,49 na safe
An gano cewa wasu filaye guda uku da Ake ginawa sun ruguje
An Fara gudanar da buncike da ceto anan take an kum gano manyan Maza uku ne suka mutu inda aka ceto wasu Maza biyu da aka samu da ransu sannan an ceto wani dattijo daya makale a karkashin baraguzun ginin inji shi
Ya Kara da cewa anyi nasarar ceto mutanan ne ta hanyar kokarin da Hukumar LASEMA da Hukumar kashe gobara ta jihar Legos ta kawo
Dukkan ma,aikata guda shidan ma,aikatan gurinne Kuma Suna samun kulawa kafin akaisu asibiti yayi da aka tuntubi sashin Kula da lafiyar muhalli na Jahar don rogowar mutane da suka mutu
Tawagar hadakan jami,an Hukumar kashe gobara dayan sanda ne aka tabbatar Suna gurinn inda suke cigaba da bada tallafi
